Zambar Naira Biliyan 1.96: Don Allah a ba ni damar tattaunawa da EFCC – Tsohon Akanta ya roki kotu

EFCC EFCC Sabo

Tsohon mukaddashin Akanta-Janar na tarayya Anamekwe Nwabuoku, wanda ke fuskantar shari’a kan zargin almundahanar Naira biliyan 1.96 a ranar Laraba, ya roki babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja da ta ba shi lokaci domin tattaunawa da hukumar yaki da masu yi wa tattalin Arzikin ƙasa ta’annati, EFCC.

Tsohon mukaddashin Akantan, wanda ke fuskantar tuhume-tuhume tara, ya yi rokon ne bayan EFCC ta bakin lauyanta, Mista Ekele Iheanacho, SAN, ya shaida wa kotun cewa ta kara kawo wasu shaidu biyar da za su ba da shaida kan lamarin.

Ko da yake lauyan mai suna Isidore Udenko ne ya wakilce shi a wurin zaman, amma wanda ake tuhumar ya shaida wa kotun cewa ya yi aiki da wani babban Lauyan Najeriya, SAN, wanda zai taimaka masa wajen sasanta lamarin a wajen kotu.

Udenko ya ce, an ci gaba da shari’ar ne bayan yunkurin farko na wanda ake kara na cimma yarjejeniya da hukumar yaki da cin hanci da rashawa, ya ci tura.

A nasa bangaren, lauyan EFCC, Iheanacho, SAN, ya ce baya adawa da bukatar wanda ake kara.

Lauyan mai gabatar da kara ya kara da cewa “Duk da cewa shaidun mu guda biyar suna gaban kotu kuma a shirye muke mu ci gaba da shari’ar, amma idan bukatar wanda ake kara za ta yi daidai da shari’ar, ba za mu yi adawa ba.”

Sakamakon haka, mai shari’a James Omotosho ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 13 ga Maris.

Alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraren karar saboda ko dai a samu rahoton sulhu ko kuma a ci gaba da sauraren karar.

Idan dai ba a manta ba, a watan Mayun 2022 ne aka nada Nwabuoku a matsayin mai kula da ofishin Akanta Janar na kasa (OAGF) na wani dan lokaci, bayan da aka dakatar da AGF na wancan lokaci Ahmed Idris daga mukaminsa, inda daga karshe aka gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zargin karkatar da kudaden jama’a da suka kai kimanin Naira biliyan 80.2.

Karanta: Zargin ɓata suna: Sanata Natasha ta maka Akpabio a kotu, tare da nema Naira biliyan 100.3 na shigar da ƙara 

Bincike kan zargin ya kai ga tsige shi daga ofishin a watan Yulin 2022, makonni kadan bayan nada shi.

Daga bisani an gurfanar da shi gaban kotu tare da wani Darakta a ma’aikatan gwamnatin tarayya, Felix Nweke.

Sai dai daga baya EFCC ta gyara tuhumar tare da cire Nweke a matsayin wanda ake tuhuma na 2 bayan ya amince ya bayar da shaida a kan tsohon mukaddashin AGF.

A cikin tuhumar da aka yi wa kwaskwarima mai lamba: FHC/ABJ/CR/240/24, EFCC ta yi zargin cewa Nwabuoku ya aikata laifin da ya saba wa sashe na 18 na dokar haramta safarar kudade ta shekarar 2011, kamar yadda doka mai lamba 1 ta shekarar 2012 ta yi wa kwaskwarima, kuma mai hukunci a karkashin sashe na 15(3) na wannan doka.

A baya dai kotun ta saurari yadda wanda ake tuhumar ya yi amfani da kamfanoni daban-daban guda hudu wajen wawure kudaden jama’a har kusan Naira biliyan 1.96.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here