Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi ya nemi diyya Naira biliyan 5 da neman gafara a fili daga dan wasan kwaikwayo da ya koma siyasa Kenneth Okonkwo kan zargin maganganun batanci da ya yi a wata hira da talabijin.
Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya kuma yi barazanar kai karar Okonkwo kotu, inds ya bayyans cewa zai iya neman diyya da tafi wannan idan ba a cika bukatunsa ba.
A cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 9 ga Yuni 2026, lauyoyin Obi karkashin Alex Ejesieme SAN, sun zargi Okonkwo da yin zarge-zarge karya, cin fuska da batanci ga wanda suke yi wa aiki a wata tattaunawa a shiirin Sunrise Daily gidan talabijin na Channels a ranar Litinin 8 ga Yuni.
Gun gun lauyoyin sun ce an buga maganganun, sannan kuma kafafen yada labarai da shafukan yanar gizo da dama suka yada su.
Bisa ga wasikar, Okonkwo ya ce “Obi, tare da shugabannin jam’iyyar NDC a Kudu maso Gabas, sun shaida wa ‘yan takarar jam’iyyar cewa duk wanda ke son takara a matsayin dan Majalisar Wakilai dole ne ya biya kudaden takara da aka tsara, sai kuma ya biya cin hanci Naira Miliyan 10 ga NDC da jagororin jam’iyyar.”
Lauyoyin sun kuma zargi Okonkwo da cewa akwai takardun shaida na biyan kudin, cewa Obi da kansa ya tattara jerin sunayen ‘yan takarar jam’iyyar daga dakin otal, ya gargadi ‘yan takara cewa Obi zai yaudare su, ya karbi kudi daga mutane waje kuma yana da hannu cikin laifuka tare da sauran shugabannin jam’iyyar.
Wasikar ta ce zarge-zargen sun nuna Obi a matsayin wanda ke da hannu cikin cin hanci, karbar kudi da karfi, zamba, rashin gaskiya da laifuka.
“Maganganun da ke sama, bisa ma’ana ta gaske da kuma abin da suke nufi, sun nuna muke yi wa aiki a matsayin wanda ke neman shirya karbar cin hanci, karbar kudi da karfi, zamba da yaudaran ‘yan takara, mazambaci nr, mai yaudara kuma dan siyasa mara gaskiya, ya hada baki da wasu yana shirya laifuka yana kuma aiwatar da laifuka,” in ji wasikar.
Lauyoyin Obin sun bayyana zarge-zargen a matsayin na karya, mara tushe, na cin fuska, sakaci, batanci da ba su da wata hujja.”
Sun ce maganganun sun wuce sharhin siyasa sun kuma zama kai tsaye hari kan mutuncin Obi da martabarsa a jama’a.
Lauyoyin sun bukaci Okonkwo, cikin kwana 7 daga ranar da ya karbar wasikar, ya janye maganganun, ya buga neman gafara da babu shakka kuma ba tare da ajiyar baki ba, sannan ya tabbatar neman gafarar ta sami daukaka daidai ko sama da yadda aka buga maganganun farko.
Bukatar ta kara da cewa: “a biya abokin harkar mu da muke yi wa aiki ta hanyar ofishin mu, kudi Naira Biliyan Biyar a matsayin diyya mai karfi da hmummunar rauni da aka yi wa mutuncinsa, dabi’arsa da matsayinsa a jama’a sakamakon maganganun karya, mugunta da batanci; sannan
Wasikar ta gargadi cewa idan ba a cika bukatun cikin lokacin da aka bayar ba, Obi bashi da wani zabin sai ya nemi mafita a kotu, ciki har da neman diyya, dokar hana yin haka, da biya kudin da ya kashe a harkar shari’a.
Da ya mayar da martani a cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, Okonkwo ya yi watsi da bukatar kuma ya ce bai karanta wasikar ba tukuna.
“An sanar da ni cewa akwai wasika da ke yawo a yanar gizo daga munafiki, Peter Obi, da lauyoyinsa da ke cewa in biya shi Naira biliyan 5, Hahaha! Idan Peter Obi yana neman kudi don yakin neman zabe, ya tambaye ni a sirrance in taimaka masa, ba daga karbar kudi da karfi ba, kuma zan taimaka masa,” in ji shi Okonkwo ya ce zai mayar da martani bisa ka’ida bayan ya duba wasikar.












































