‘Yan bindiga sun sace mataimakin shugaban karamar hukuma

Gunmen

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai farmaki Ora-Igbomina a Karamar Hukumar Ifedayo ta Jihar Osun, inda suka sace mataimakin shugaban karamar hukumar, Debo Faroumbi.

Rahotannin da aka tattara sun ce ‘yan bindigar sun mamaye garin cikin dare a ranar Talata, inda suka dinga harba bindiga sama-sama da nufin firgita mutanen garin.

An kuma rawaito cewa ‘yan bindigar sun kama mutane 4, ciki har da mata 2 ‘yan Fulani da wani mutum daya sai kumaMr Faroumbi.

Sai dai cikin gaggawa sojojin da ke garin suka fuskanci ‘yan bindigar, inda suka bi su ba tare da gajiyawa ba, lamarin da ya tilasta musu su barin 3 daga cikin wadanda suka sace yayin da suka gudu da jami’in karamar hukumar zuwa cikin daji.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar Osun, Abiodun Ojelabi ya ce ‘yan sanda sun fara bin diddigin ‘yan bindigar domin ceto wanda aka sace.

“Eh, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun mamaye Ora-Igbomina a Karamar Hukumar Ifedayo, inda suka sace mutane 4, amma sojoji sun tilasta musu barin 3 daga cikin wadanda aka sace.

“Sun samu nasar tafi da Debo Faroumbi zuwa daji tare da su, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun fara bin diddigin ‘yan bindigar,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here