Dakarun sojin Najeriya dake bataliya ta 34 sun kashe wani dan bindiga da aka gano shi ne kwamandan kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra IPOB a jihar Imo.
Dakarun sun yi musayar wuta da mambobin kungiyar ta IPOB, inda su kai ta yin harbi kan mai uwa da wabi a mahadar Banana dake karamar hukumar Orlu.
Ana zargin ‘Yan kungiyar IPOB din da tursasawa al’umma bin dokarsu da suka sanya wajen zaman dole a gida.
A sanarwar da mai Magana da yawun rundunar sojin Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar ranar Litinin a Abuja, ya ce dan bindigar ya mutu ne yayin dauki ba dadin.
Nwachukwu ya ce a lokacin da Yan kungiyar IPOB din suka ga sojojin, sun gudu a cikin wata mota kirar Toyota Highlander zuwa yankin Ihioma domin karfafa musu gwiwa.
“A Yayin musayar wutar da muka yi dasu, daya daga cikin yan ta’addar ya kwanta dama, yayin da wasu suka gudu da raunuka a jikinsu.
Yanzu haka Sojoji suna ci gaba da yin rangadi a yankin gaba daya a wani mataki na ci gaba da zakulo ‘yan ta’addar da suka tsere.”
“Bayan sun sha da kyar, kungiyar ta yi amfani da farfaganda don tayar da hankulan jama’a.
“Sun yi ta yada wani faifan bidiyo a kafafen sada zumunta a cikin Faifan Bidiyon suna zargin sojojin da hannu wajen aikata ta’asar da suke yi.
Ya kamata a yi watsi da wannan farfagandar gaba dayanta,” in ji sanarwar.













































