Matasa su shirya wa damar da za su samu, su jagoranci kirkire-kirkire don cigaban kasa – Kole Shettima

Kole Shettima new

Darakta na Ofishin Gidauniyar MacArthur a Najeriya kuma Babban Daraktan Shirin “On Nigeria”, Dr. Kole Shettima ya bukaci matasan Najeriya su shirya kansu domin damar da za su samu ta hanyar kwazo, kirkire-kirkire da ci gaba da koyon abubuwa, inda ya jaddada cewa basira kadai baza ta isa ba wajen tabbatar da nasara.

Da yake gabatar da jawabin bude taron “Northeast Youth Idea Summit” karo na 2 da aka gudanar a Damaturu, Jihar Yobe, a ranar Asabar, Dr. Shettima ya ja hankalin matasa su samar da mafita mai amfani ga matsalolin al’umma kuma su tsara kansu domin su samun damar da za ta taso a kowane lokaci.

A cewar sa, bambancin da ke tsakanin wadanda suka samu nasara da sauran hazikai da dama, galibi damar da suka samu ce ba basira ko iyawa ba.

Ya ba da misali da rayuwar sa daga Machina a Jihar Yobe har ya samu tallafin karatu na PhD a Jami’ar Toronto, Kanada, Dr. Shettima ya ce nasararsa ta tabbata ne saboda wani ya gane hazakar sa ya tallafa masa saboda ya samu gobe mai kyau.

“Bambancin da ke tsakanin ni da yawancin abokan karatuna, dama ce kawai. Ina da tabbacin da yawa daga cikinsu suna da hazaka kamar ni, amma wani ya ga hazakar ta ya ba ni tallafin karatu,” in ji shi.

Ya karfafi mahalarta taron da kada su dogara da sa’a, yana mai bayanin cewa nasara na zuwa ne idan shiri ya hadu da dama.

“Mutane suna cewa wani ya yi sa’a, amma sa’a kawai na nufin ka kasance a shirye lokacin da dama ta zo. Ba za ka iya amfani da damar ba idan ba ka shirya ba,” in ji shi.

Shettima, kwararre a bangaren cigaba, ya kuma kalubalanci matasa kan su samar da mafita ta hanyar amfani da fasaha da kirkire-kirkire wajen magance matsalolin cigaban Najeriya maimakon kawai yin kalubale.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here