Kotu ta soke hukuncin da ya amince da NDC a matsayin jam’iyyar siyasa

NDC NDC

Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ta soke hukuncin ta na baya da ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi wa jam’iyyar NDC rajista a matsayin jam’iyya siyasa. Wannan ya soke dukkan ayyukan da aka yi bisa hukuncin.

Mai Shari’a Isah Dashen ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a, ya ce hukuncin Kotun na ranar 10 ga Disamba, 2025 ya shafi hakin jam’iyyar PMP, wadda ba a shigar da ita cikin karar ba duk da cewa tana da’awar mallakar tambarin da aka dogara da shi wajen samun hukuncin.

Lauyan mai jam’iyyar PMP mai kara, C. S. Ekeocha, ya shaida wa ‘yan jarida cewa PMP ta kai kara kotu ne bayan ta gano cewa rajistar NDC ta dogara ne kan tambarin da ta tura wa INEC kafin a fara karar.

A cewar Ekeocha, kotun ta yarda cewa an shafi hakin mai karar, saboda haka ta soke hukuncin da ta yi a baya.

“Kotun ta umarci dukkan bangarorin su koma inda suke kafin hukuncin 10 ga Disamba, 2025, kuma ta umarci masu kara su shigar da dukkan bangarorin da suka dace domin a warware matsalar gaba daya,” in ji shi.

Ya bayyana cewa ma’anar hukuncin shi ne duk abin da INEC ta yi bisa hukuncin da aka soke yanzu ya zama mara amfani.

”Ya kamata a janye amincewar da aka baiwa NDC da kuma shaidar rajista da shigar da ita cikin rajistar INEC da duk wata bayyana sunanta a takardar zabe da aka yi sakamakon hukuncin, har sai an kammala karar gaba daya,” in ji Ekeocha.

Sai dai ya bayyana cewa babbar karar na nan gaban kotu kuma ba a yanke hukunci ba tukuna.

”Ba a kammala lamarin ba. Kotun kawai ta soke hukuncin ta na baya kuma ta umarci a shigar da jam’iyyar da ke da haki, domin a saurari kowa kafin a yanke sabon hukunci.”

Ekeocha ya kuma musanta rahotannin da ke cewa kotun a tsaya a yadda ake a halin yanzu. Ya ce hukuncin ya umarci a dawo halin da ake ciki kafin hukuncin 10 ga Disamba, 2025.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here