Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta yanke na rushe ƙunshin shugabannin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC da Kuma zaɓen ƙananan hukumomi da hukumar ta gudanar a ranar 26 ga Oktoban shekarar 2024.
A cikin hukunce-hukunce guda uku, wadda kotun mai alƙalai uku ta yanke wanda mai shari’a Biobele Georgewill ya jagoranta, ya bayyana cewa kotun ta baya ba ta da hurumin gudanar da shari’o’in da ke da alaka da kunshin hukumomin zabe na jihohi da kuma cancantar mambobin irin wadannan hukumomin.
Kotun daukaka karar ta kuma amince da kararraki uku da Babban Lauyan Jihar Kano, da Majalisar Dokokin jihar Kano da hukumar KANSIEC suka shigar, inda ta yi watsi da karar da aka shigar gaban babbar kotun tarayya da ke neman samun hurumin soke zaɓen tare da bayyana cewa babbar kotun jihar Kano ce ke da hurumin sauraron shari’ar ba wai ta tarayya ba.
Kotun daukaka ƙarar ta kuma soke wani hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Kano ta yanke, inda ta yi watsi da jerin sunayen ‘yan takarar da bangaren Rabi’u Musa Kwakwanso na jam’iyyar NNPP ya mika wa KANSIEC a zaben kananan hukumomin jihar Kano da ya gabata.













































