A yau Juma’a ne Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta tura sabbin kwamishinonin zabe na jihohi watau RECs, domin cike giɓi a jihohi 6 da babu shugabannin.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, an tura wadannan shugabanni guda shida ne jim kadan bayan rantsar da su a shalkwatar hukumar ta INEC da ke Abuja.
Sabbin shugabannin sun hada da Dakta Sa’ad Idris da Dakta Johnson Sinikiem sai Feyijimi Ibiyemi da Mukhtar Gajiram da Chukwuemeka Ibeziako da kuma Umar Garba.
Haka kuma ta ruwaito cewa, an tura Dakta Sa’ad Idris zuwa Gombe sai Dakta Johnson Sinikiem zuwa Cross River Feyijimi Ibiyemi zuwa Ogun, Mukhtar Gajiram zuwa Taraba, ChukwuemekaI beziako zuwa Abia sai kuma Umar Garba da aka tura shi Sokoto.
Da ya ke jawabi yayin rantsar da su, Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, an cike dukkan dukkan shalkwatocin jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya da shugabannin hukumar.
Yakubu ya bukace su da su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata kuma bisa gaskiya da adalci.













































