Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, wanda kuma shi ne sabon shugaban hukumar kula da fina-finai ta Kasa, Ali Nuhu ya ce zai mayar da hankali kan wasu manyan sauye-sauye guda 3 a hukumar da zai jagoranta.
Karanta wannan: Naira ta ragu zuwa 1,500 a kasuwar canjin kudade
A watan da ya gabata ne dai shugaba Bola Tinubu ya nada shi a matsayin shugaban hukumar.
Za’a iya cewa dai Ali Nuhu ne jarumi na farko daga arewacin Najeriya da ya samu irin wannan dama ta jagorantar hukumar da ke kula da masana’antar da ya fito daga cikinta.