Sanannan masani a fannin likitancin dabbobi da gudanar da jami’a Farfesa AbdulGaniyu Ambali ya rasu da safiyar Asabar a gidansa da ke Oloje Estate, Ilorin, babban birnin Jihar Kwara.
Daraktan Harkokin Jama’a na jami’ar, Kunle Akogun ne ya tabbatar da rasuwar a cikin wata sanarwa. Inda ya ce Shugaban Jami’ar Ilorin, Farfesa Wahab Olasupo Egbewole, SAN, ya sanar da rasuwar shugaban jami’ar na 9, Farfesa AbdulGaniyu Ambali, OON.
Sanarwar ta ce, “Farfesa Ambali, wanda ya jagoranci Jami’ar daga ahekarar 2012 zuwa 2017, ya rasu da safiyar yau bayan rashin lafiya ta dan lokaci yana da shekaru 68.
“Rasuwar Farfesa Ambali, a cewar Shugaban, babbar asara ce ba kawai ga Jami’ar Ilorin da Jami’ar Jihar Kwara da ke Malete, wadda yanzu haka yake hidima a matsayin Shugaban Majalisar Gudanarwa ba, rashi ne ga kasa da al-umma baki daya
“Farfesa Egbewole, wanda ya ta’aziyya wa iyalin babban malamin da al-ummar Masarautar Ilorin, ya bukaci masu ta’aziyya, musamman mambobin al’ummar UNILORIN, su halarci sallar Janaza ta marigayi tsohon shugaban a gidansa na Oloje Housing Estate, Ilorin, da karfe 4 na yamma yau, Asabar 6 ga Yuni 2026.”
Kafin rasuwarsa, Ambali shi ne Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami’ar Jihar Kwara, matsayin da ya rike bayan kammala wa’adinsa a Jami’ar Ilorin.
An haifi marigayi malamin a ranar 29 ga Nuwamba1957, a Ilorin, Jihar Kwara, inda ya fara karatunsa a Makarantar Firamare ta Pakata kafin ya shiga Makarantar Sakandare ta Gwamnati, Jalingo.
Ya samu digirin Likitan Dabbobi DVM daga Jami’ar Ahmadu Bello a 1981 sannan daga baya ya samu digiri na biyu da na uku PhD a fannin Likitancin Dabbobi daga Jami’ar Liverpool.
Ya yi lacca a Jami’ar Maiduguri kafin ya koma Jami’ar Ilorin, inda ya hau matakai har ya zama Farfesa na Likitancin Dabbobi sannan daga baya ya zama Shugaban Kwalejin Likitancin Dabbobi na farko.
Ambali ya kuma taba zama Shugaban Kungiyar Jami’o’in Yammacin Afirka kuma Mabiyi na Kwalejin Likitocin Dabbobi ta Najeriya.












































