Hukumar kula da yanayi ta kasa NiMET ta yi hasashen cewa za a samu ƙwallewar hasken rana da gizagizai daga ranar Litinin zuwa Laraba a sassan ƙasar nan.
Rahoton yanayin da hukumar ta fitar ya nuna cewa a yankin arewa za a samu sararin sama mai hasken rana tare da gizagizai a tsawon lokacin hasashen, ba tare da manyan sauye-sauye ba.
A yankin kudu kuma, hasashen ya nuna za a ga hasken rana tare da wasu gizagizai, tare da yiwuwar saukar ruwan sama kaɗan da tsawa a wasu sassan jihohin Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom da Cross River a ƙarshen rana.
A ranar Talata, hukumar ta nuna cewa yankunan arewa da tsakiyar ƙasa za su fuskanci hasken rana mai gauraye da hazo, yayin da yankin kudu zai ci gaba da samun hasken rana tare da gizagizai, tare da yiwuwar tsawa da ruwan sama kaɗan a wasu jihohi da dama da suka haɗa da Lagos, Ogun, Rivers, Bayelsa, Akwa Ibom da Cross River da safe, sannan daga baya a rana a ƙara samun tsawa a wasu jihohi.
Hasashen ranar Laraba ya nuna cewa yankin arewa zai samu hasken rana mai hazo da kuma kura a cikin rana, yayin da yankin tsakiyar ƙasa zai kasance cikin yanayi makamancin haka, amma a kudu ana sa ran gizagizai da hasken rana a safiya tare da yiwuwar tsawa da ruwan sama kaɗan a wasu jihohi.
Hukumar ta gargadi jama’a, musamman masu fama da cututtukan numfashi, da su kula da kansu saboda hazo da kura, tare da jan hankalin direbobi da su yi taka-tsantsan yayin tuƙi a lokacin ruwan sama.
Sannan ta shawarci kamfanonin jiragen sama su rika neman cikakkun bayanan yanayi domin tsara ayyukansu yadda ya dace.
NAN













































