Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya karɓi wata tawaga daga ƙasar Amurka a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda taron ya gudana a Aso Rock domin tattauna batutuwan da suka shafi tsaro da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.
Tawagar ta zo ne ƙarƙashin jagorancin Janar Dagvin R. Anderson, kwamandan rundunar sojojin Amurka a nahiyar Afirka, tare da mukaddashin jakadan ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, Keith Heffern, da sauran jami’an tawagar.
Taron ya gudana a fadar gwamnati, inda shugaban ƙasa ya tarbi baƙin tare da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu, da kuma shugabannin rundunonin tsaron ƙasar.
Wata sanarwa daga mataimakin shugaban ƙasa kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun, ta bayyana cewa shugaban ƙasa tare da mai ba shi shawara kan tsaro da shugabannin rundunoni sun karɓi kwamandan rundunar sojojin Amurka a Afirka da tawagarsa a fadar gwamnati da ke Abuja.
Ko da yake ba a fitar da cikakkun bayanai kan abin da aka tattauna a taron na sirri ba, ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ake ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da ƙasar Amurka.
Ziyarar ta kuma biyo bayan rahotannin da suka nuna cewa ƙasar Amurka ta turo ƙaramin tawagar sojoji zuwa Najeriya a farkon watan Fabrairu, lamarin da ya nuna dawowar sojojin Amurka ƙasar bayan hare-haren sama da aka kai kan wuraren ’yan ta’adda a ƙarshen shekarar da ta gabata.













































