Kungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC ta yi gargaɗin yiwuwar gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya da kuma kaurace wa zaɓe, bisa abin da ta bayyana a matsayin ruɗani da sabanin matsayi daga Majalisar Dattawa dangane da gyare-gyaren dokar zaɓe, musamman kan batun tura sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki.
Kungiyar ta zargi Majalisar Dattawa da raunana amincewar jama’a ga tsarin zaɓen Najeriya, sakamakon gazawarta wajen fayyace ko tura sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki zai zama tilas ko a’a, lamarin da ta ce yana jefa al’umma cikin rashin tabbas.
Kungiyar ƙwadagon ta bayyana cewa rashin fayyacwa game da matsayar ƙarshe da Majalisar Dattawa ta ɗauka na barazana ga sahihancin zaɓe da amincewar jama’a, tare da jaddada cewa ‘yan Najeriya sun cancanci tsarin da yake a bayyane, inda ba kawai ana ƙirga ƙuri’u ba, har ma jama’a ke ganin yadda ake ƙirga su.
Ta nuna cewa bayanan da ke fili sun nuna cewa an ƙi amincewa da gyaran da zai tilasta wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa tura sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki kai tsaye a lokacin ƙirga su, inda aka bar tanadin da ke bai wa hukumar damar zaɓar yadda za a tura sakamakon, abin da ya haddasa fargaba a faɗin ƙasar tare da ƙara ruɗani sakamakon bayanan da suka biyo baya.
Kungiyar ta buƙaci Majalisar Dattawa ta fitar da cikakken bayani na hukuma ba tare da shubuha ba, kan ainihin tanade-tanaden da aka amince da su a ƙarshe, ciki har da rubutaccen tsari na ƙarshe da dalilan da suka sa aka yanke irin wannan hukunci, domin duk wata shubuha a wannan muhimmin lokaci bayan babban zaɓen ƙasa na iya ƙarfafa shakku a tsarin zaɓe.
Kungiyar ƙwadagon ta dage cewa dole ne dokar zaɓe da aka gyara ta tanadi umarni karara da zai tilasta wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa turawa da tattara sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki daga rumfunan zaɓe kai tsaye, tana gargaɗin cewa rashin yin hakan na iya jawo ɗaukar matakin gama-kai kafin zaɓe, a lokacin zaɓe da kuma bayan zaɓe, ko kuma kaurace wa zaɓen gaba ɗaya.
Ta ƙara da cewa al’ummar ƙasar da ma’aikata na sa ido sosai, tare da kira ga ƙasar da ta zaɓi tafarkin gaskiya da mutunci, tana buƙatar kauce wa irin ruɗanin da ya biyo bayan sababbin dokokin haraji, tare da cewa lokaci ya yi na samar da dokoki masu gaskiya da suka sanya muradin jama’a a gaba.













































