A ranar Alhamis ne gidauniyar WOFAN ta kaddamar da cibiyar sana’o’i ga mata da masu bukata ta musamman tare da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana a yankin Kudai dake jihar Jigawa.
Haka kuma WOFAN ta raba baburan daukar kaya masu kafa uku guda 24, don amfanin masu safarar kayayyakin amfanin gona, da kuma kekunan guragu 40.