Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya gargadi Kungiyar tsaron arewacin tekun Atlantika cewa makoma mara kyau na iya jiran kungiyar idan kasashen kawancenta ba su taimaka wajen bude mashigar Hormuz ba, tare da cewa zai iya jinkirta wani taron koli da aka shirya yi da shugaban kasar China, Xi Jinping.
Trump ya bayyana cewa yana ganin ya dace China ma ta taimaka saboda yawancin man fetur da kasar ke amfani da shi yana wucewa ta mashigar Hormuz, yana mai cewa zai fi so ya san matsayar Beijing kafin ziyarar da aka shirya yi.
Sakataren baitul malin Amurka, Scott Bessent, da mataimakin firaministan China, He Lifeng, sun kammala rana ta farko cikin kwanaki biyu na tattaunawa a Paris domin magance sabanin da ke cikin yarjejeniyar dakatar da takaddamar kasuwanci tsakanin kasashen biyu da kuma share fagen ziyarar Trump zuwa Beijing domin ganawa da Xi a karshen watan Maris.
Shugaban na Amurka ya bayyana cewa kasashen da ke cin moriyar wannan hanyar jiragen ruwa su ma ya dace su taimaka wajen kare ta.
Trump ya kuma bukaci kasashe su tura jiragen ruwan yaki domin tabbatar da cewa mashigar ruwa ta ci gaba da kasancewa a bude ga zirga-zirgar jiragen ruwa, yayin da dakarun Iran ke ci gaba da kai hare-hare bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran.
Ya bayyana cewa yana sa ran kasashe kamar China da Faransa da Japan da Koriya ta Kudu da kuma Birtaniya za su tura jiragen ruwa zuwa yankin.
Trump ya ce taimakon da ake bukata na iya hada da jiragen da ke gano da kuma kawar da nakiyoyin ruwa da sauran kayan aikin soja domin dakile jiragen marasa matuka da nakiyoyin ruwa.
Iran ta rufe mashigar Hormuz bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai mata sama da makonni biyu da suka gabata. Kimanin kashi daya cikin biyar na man fetur da iskar gas mai ruwa da ake safararsa a duniya kan wuce ta wannan mashiga ta ruwa dake tsakanin Iran da Oman.
Trump ya kuma yi gargadin cewa Amurka na iya kai wasu karin hare-hare kan tsibirin Kharg Island, wuri mafi girma da Iran ke fitar da man fetur, yana cewa dakarun Amurka na iya kai hari kan cibiyoyin man fetur idan bukatar hakan ta taso.
Ya kuma soki martanin Birtaniya bayan tattaunawarsa da firaministan kasar, Keir Starmer, yana cewa duk da cewa Birtaniya na daga cikin manyan kawancen Amurka, ba ta gaggauta amincewa da tura jiragen ruwa ba sai bayan Amurka ta rage karfin sojan Iran.












































