Wata hadaka ta kungiyoyin fararen hula da kungiyoyin al’umma ta bukaci majalisar dokokin Jihar Jigawa ta gudanar da bincike kan zargin rashin kyakkyawan tafiyar da kudade a kananan hukumomin jihar.
Kungiyoyin fararen hula da kungiyoyin al’umma karkashin hadakar hadin gwiwar tabbatar da shigar jama’a cikin tafiyar da mulkin kananan hukumomi sun bayyana wannan bukata a cikin wata sanarwa da sakataren janar na hadakar, Ibrahim Ilallah, ya fitar a Dutse.
Kungiyar ta bayyana cewa ta lura sosai da rahotanni da tattaunawar jama’a da ake yi a kafafen sadarwar zamani dangane da zargin karkatar da kudade, rike kudaden kananan hukumomi ba bisa ka’ida ba, cire wasu kudade daga rabon kudaden kananan hukumomi ba bisa doka ba, da sauran matsalolin kudi da ke shafar kananan hukumomin jihar.
Ilallah ya bukaci kakakin majalisar dokokin jihar, Haruna Dangyatin, da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya bai wa majalisar domin tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da kudaden kananan hukumomi.
Ya yi nuni da sashe na Bakwai na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima, wanda ya bai wa majalisun dokokin jihohi iko na tabbatar da ingantaccen tsari, tsarin shugabanci, kudade da kuma yadda zababbun shugabannin kananan hukumomi ke gudanar da ayyukansu.
Ya kara da cewa aikin sa ido na majalisar na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana a yadda ake tafiyar da dukiyar jama’a a matakin kananan hukumomi.
A cewarsa, wannan alhaki ya hada da binciken duk wani zargi na cin hanci, rashin inganci ko kuma amfani da mukami ba daidai ba idan bukatar hakan ta taso.
Hadakar ta kungiyoyi ta kuma bayyana cewa amsa cikin gaggawa da kuma a bayyane ga wannan kira zai kara karfafa amincewar jama’a ga majalisar dokokin jihar Jigawa.










































