Jirgin saman Jihar Kano zai fara aiki shekara mai zuwa – Gwamna Yusuf

Abba Kabir Yusuf Airline 750x430

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana shirin gwamnatinsa na kafa kamfanin jirgin sama na kasuwanci mallakar jihar wanda ke da manufar samar da ayyukan yi kai tsaye ga jama’ar jihar ta Kano da suka kammala karbar horon kan tuka jirgi.

Wannan na cikin sanarwar da Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis.

Gwamna Yusuf ya sanar da hakan ne a yayin taron Majalisar Zartarwa na 40 da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano, inda aka ba shi lambobin yabo da dama, ciki har da lambar yabo daga Kungiyar Matukan Jirgin Sama ta Jihar Kano bisa jajircewarsa wajen tallafawa mambobin kungiyar domin kammala horon su na jirgin sama.

Gwamnan ya bayyana cewa, da yardar Allah, ana sa ran sabon jirgin saman mallakin jihar Kano zai fara aiki cikin shekara mai zuwa.

Ya tabbatar wa mambobin kungiyar cewa gwamnatin jihar za ta ba da dukkanin tallafin da ake bukata domin tabbatar da cewa an kammala aikin tare da tabbatar da jirgin ya fara aiki cikin nasara.

Gwamna Yusuf ya kuma nuna jin dadinsa kan yadda matukan jirgin da gwamnatin Kano ta dauki nauyin horar da su a Jordan suka yi fice a karatunsu, a shiri da gwamnatin da ta gabata ta fara.

Tun da fari, shugaban kungiyar Matukan Jirgin Saman ta Jihar Kano, Naziru Ibrahim, ya yaba wa Gwamna Yusuf kan ci gaba da tallafawa, musamman wajen saukaka sabunta lasisin tuka jirgi na mambobin kungiyar.

Ya kuma roki Gwamnan da ya kara taimaka wa matukan jirgin wajen samun takardun kammala horo na karshe, wanda zai ba su damar tuka jirage na kasuwanci a cikin Najeriya da ma na kasashen waje.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here