Daga Halima Lukman
Kungiyar Wutan lantarki na TCN, Ta ce ma’aikatan ta na aiki dare da rana domin gyara Wutan lantarki.
Inda TCN ta bayyana cewa zuwa 27 ga watan mayu tana sa ran gama gyaran Wutan.
SolaceBase ta tattauna da Al’uman garin kashere game da rashin Wutan lantarki da ke addabar su.
Mal Sulaiman Abubakar, mai siyar da kayan sanyi ya bayyana wa jaridar Solacebase
Cewa kasuwan cinsu ya ragu, Saboda ada suna sarar da lemun kwalba Amma yanzu masu shagunan ma basa siya Saboda rashin wuta, Mal Sulaiman ya kare da cewa ya siyar da Rabin shagon shin domin siyan injin din gas. Da ga karshe yace baitabbatar idan zasu gyara Wutan ba nan kusa.
Malam Idris mai chajin waya, ya shedawa SolaceBase cewa Kullun sai sun je gurin mai Nisa kafin su samu man fetur Saboda Rashin wuta ga tsadan mai. Hakan yasa suke karban 150 na chajin waya (android) 300 na power bank, 600 na laptop.
Haka zalika daliban jami’ar tarraya ta kashere suma sun koka kan rashin wutar, inda suke cewa dana abinci zasu ji ko da saka chaji, gashi caji yayi tsada.