‘Yan ta’adda sun kai hari makaranta a Borno, sun sace daliban da ke rubuta NECO

Borno map

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Borno ta tura jami’an tsaro zuwa garin Lassa dake Karamar Hukumar Askira/Uba bayan da wasu ‘yan ta’adda da ake zargi sun sace dalibai da ba a kai ga tabbatar da adadin yawan su ba, wadanda ke rubuta jarabawar kammala sakandire ta Kasa NECO.

An bayyana cewa maharan sun mamaye makarantar da misalin karfe 9 na safe a ranar Litinin, inda suka yi harbe-harbe da bindiga a sama kafin su sace dalibai da mata da ke sayar da abinci a cikin makarantar.

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin ‘yan sandan jihar Borno, Nahum Daso, ya ce jami’an tsaro sun fuskanci maharan, wanda hakan ya hana su sace adadi mai yawa.

“Da misalin karfe 9 na safe, ISWAP ta kai hari Makarantar Sakandaren jeka ka dawo ta Lassa. Sun yi harbe-harbe da bindiga kafin su sace dalibai da ba a tabbatar da yawan su ba.

“Jami’an tsaro sun fuskance su, muna da adadin dalibai da ba a tabbatar da yawan su ba da aka sace. Kwamishinan ‘Yan Sanda ya tura runduna yankin Askira/Uba.” in ji Daso.

Mai baiwa gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, shawara a bangaren yada Labarai da dabaru, Mista Solomon Kwamagar, wanda dan asalin Lassa ne, ya kuma tabbatar da lamarin a safiyar ranar Litinin.

Ya bayyana cewa maharan sun zo ne da babura suka mamaye makarantar.

“A yau kasuwar Lassa ke ci, an sanar da ni cewa sun zo ta kasuwa ne da babura suka je makarantar gwamnati ta jeka ka dawo Lassa. Sun yi harbi tare da kashe malami daya suka kuma tafi da dukkan daliban da suke cikin ajujuwa,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “Har yanzu ina tuntubar mutane don tabbatar da adadin dalibai da malamai da aka sace daga makarantar.”

A baya can, Shugaban Kungiyar Matasan Borno ta Kudu, Samaila Kaigama, ya shaida wa manema labarai cewa maharan sun sa tufafin soja da na masu kare dazuka.

“Haka ne, an kai hari kan daliban da ke rubuta jarabawar NECO. ‘Yan ta’addan sun zo da misalin karfe tara da wani abu, sun wuce sansanin sojoji. Sun sa tufafin soja da na masu kare daji. Sun harba bindiga kan mai uwa da wabi,” in ji shi.

Kaigama ya ce an kashe malami daya yayin da wani ya samu raunin harbin bindiga.

Idan za a iya tuna a ranar 16 ga watan Mayu, an sace dalibai 42 bayan da wasu ‘yan Boko Haram da ake zargi suka kai hari Makarantar Firamare da Sakandare ta Junior Mussa da ke Karamar Hukumar Askira/Uba.

Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ce wadanda aka sace sun hada da dalibai hudu na Makarantar Gwamnati ta jeka ka dawo, daliban firamare 28 da yara 10 da aka sace daga gidajensu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here