Hukumar Kiyaye Hadura ta tabbatar da mutuwar mutum 15, yayin da 25 suka jikkata a hatsarin mota a Neja

Accident new

Kwamandan Hukumar Kula da Kare Haddura ta Kasa (FRSC) a Jihar Neja, Aishatu Sa’adu, ta tabbatar da mutuwar matafiya 15, yayin da aka garzaya da wasu 25 zuwa asibiti biyo bayan wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan titin Enagi zuwa Mokwa.

Yayin da take jawabi ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Lahadi a garin Minna, Kwamandan rundunar ta bayyana cewa hatsarin ya ritsa da motocin safa guda biyu da ke tafe ta hannu guda.

A cewarta, mutum 15 ne suka kone kurmus lokacin da gobara ta tashi a motocin bayan sun yi karo da juna da yammacin ranar Asabar.

Ta kara da cewa an garzaya da sauran fasinjoji 25 da suka samu raunuka zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya dake Bida da Babban Asibitin Kutigi domin jinya.

Sa’adu ta danganta hatsarin da gudun wuce kima a wurin da ke da lankwasa.

“Hatsarin ya faru ne sakamakon gudu da ya wuce kima da kuma kokarin wuce mota ba a daidai ba.
“Ina shawartar masu ababen hawa da su rika kiyaye ka’idojin gudu kuma su guji wuce motoci ta hanyar da ba ta dace ba,” in ji ta. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here