‘Yan bindigar da suka sace Jami’an Yi wa Kasa Hidima (NYSC) wadanda suka taso daga Jihar Bayelsa zuwa Abuja sun bukaci kudin fansa na naira miliyan 20 ga kowane mutum.
An sace masu yi wa kasar hidima ne kwanaki uku da suka gabata a kan hanyar Aloma Egane a Karamar Hukumar Ofu ta Jihar Kogi, bayan kammala makonni uku na karbar horo.
Wani dan uwan daya daga cikin wadanda aka sace ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun tuntubi iyalin kuma sun bukaci naira miliyan 20 domin sakin ‘yar su.
“‘Yan bindigar da suka sace ‘yarmu a hanyarta ta dawowa daga Bayelsa zuwa Abuja bayan kammala makonni uku na horo, suna neman naira miliyan 20,” in ji majiyar.
Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kogi ta tabbatar da sace-sacen, inda ta ce an sace fasinjoji da dama ciki har da Jami’an NYSC a kan wannan hanya.
Daga baya hukumar ta bayar da rahoton cewa an ceto mutane 11 da aka sace, ciki har da direbobin motoci biyu da abin ya shafa, ta hanyar wani aiki na hadin gwiwa da hukumomin tsaro suka gudanar.
Duk da haka, ana kyautata zaton wasu daga cikin jami’an NYSC da sauran fasinjoji har yanzu suna hannun ‘yan bindigar, yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da kokarin gano su da ceto su.
Iyalan wadanda aka sace sun roki Gwamnatin Tarayya, NYSC da hukumomin tsaro da su kara karfafa kokari wajen tabbatar da sakin wadanda har yanzu suke hannun ‘yan bindigar.












































