Dalibai da dama zasu ajiye karatun su sakamakon karin kudin makaranta da akai  makarantun kasar nan – Kungiya

Tertiary students
Tertiary students

Kungiyar  National Association of Academic Technologists (NAAT) ta bayyana damuwar ta bisa karin kudin makaranta da akai a manyan makarantun kasar nan.

A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, mista Mr Ibeji Nwokoma ya fitar ranar Lahadi, yace magantuwar ta su ta biyo bayan taron masu ruwa da tsaki na 52 da kungiyar ta gabatar a jimi’ar kimiya da fasaha ta Aliko Dangote dake Kano.

Ya kara da cewa magantuwar tasu ta zama dole bisa ganin yadda manyan makarantun kasar nan suka kara kudin makaranta duk da yanayin halin matsin tattalin arziki da ake fuskanta a kasar nan.

Shugaban kuma ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake duba tsarin bada lamanin karatu da aka shigu dashi, duba da yacce tsari zai yi wuya talakawa su iya kai ga samu, saboda matakan da zasu bi sunyi tsauri da yawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here