Rikicin Masarautar Kano: Kotun Koli da Gwamna Yusuf ne ke da hurumin yanke hukunci – Ganduje

Ganduje Speaking Green 2
Ganduje Speaking Green 2

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa Kotun Koli ta Najeriya ce kadai ke da hurumin yanke hukunci kan makomar Muhammadu Sanusi II a rikicin sarautar Kano da ke ci gaba.

Matakin Gwamna Abba Kabir Yusuf zai tabbatar da aiwatarwa bisa doka da oda.

Dr Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa ya amince da Sanusi a matsayin Sarkin Kano kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kano.

A cikin wata sanarwa da tsohon Kwamishinan Yada Labarai kuma Babban Shugaban Ma’aikatan Gandujen, Kwamared Muhammad Garaba ya sanya wa hannu, Dr Ganduje ya ce an yi wa rahotannin fassarar da ba daidai ba ne, kuma ambaton da ya yi wa Sanusi da sarautarsa a lokacin rantsar da Mataimakin Gwamna abu ne na ladabi da bin ka’ida kawai.

“Yana da muhimmanci a fayyace cewa abin da ya faru ladabi ne kawai da aka nuna a wajen taron jama’a, bai kamata a fassara shi a matsayin amincewa ba,” in ji shi.

Ya jaddada cewa rikicin sarautar na karkashin shari’a ne a halin yanzu, yana mai gargadin cewa a yi taka-tsantsan wajen yin sharhi a bainar jama’a domin kaucewa abin da zai kai ga wulakanta kotu.

Tsohon gwamnan ya bayyaa cewa Kotun Daukaka kara ta umarci bangarorin biyu da su ci gaba da rike matsayin da ake ciki yanzu har sai an yanke hukunci na karshe kan karar.

“Matsayin da doka ke yanzu ta yarda Aminu Ado Bayero ne Sarkin Kano na 15 yayin da Muhammadu Sanusi II ne Sarkin Kano na 14, har sai Kotun Koli ta yanke hukunci na karshe,” in ji shi.

Ya jaddada cewa, a matsayinsa na tsohon gwamna, ba shi da ikon bisa kundin tsarin kasa na amincewa ko kin amincewa da wani da ke neman sarauta, yana mai cewa al’amarin yana hannun kotu ne kawai sannan daga baya ya koma hannun gwamnatin jihar.

SolaceBase ta ruwaito cewa Dr Ganduje ya nuna nadama kan yadda wasu sassan kafafen yada labarai suka hada batun, yana mai cewa abin da zai iya zama gaisuwar da ta dace bisa ka’idar da aka riga aka kafa an kara mata girma fiye da yadda ya kamata.

“Fassarar da ake wa kalaman na kara musu girma ne kawai, ina karfafa dukkan bangarorin da su yi hakuri su jira hukuncin Kotun Koli, wanda ake sa ran za a yanke shi a watan Afrilu na shekara mai zuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here