Gwamna Yusuf ya hade ma’aikatar ruwa da ta muhalli

1780345099549 750x430

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da hade Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi zuwa ma’aikata daya, wadda za a dinga kira da Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi.

Kwamishinan sabuwar ma’aikatar da aka hade, Dr. Dahir M. Hashim ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana matakin a matsayin mai cike da dabara da aka yi domin karfafa hadin kai da inganta samar da ayyuka a fannin ruwa, muhalli da yanayi.

Dr. Hashim ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan amincewar da ya ba shi na jagorantar sabuwar ma’aikatar, yana mai alkawarin yin aiki tukuru domin cimma manufarta a madadin al’ummar Kano.

A cewarsa, hadewar ta hada bangarori biyu masu muhimmanci wadanda ayyukansu sun bambanta amma suna da alaka sosai, yana mai cewa hadewar za ta bukaci sadaukarwa, tsari mai inganci, da aiki tukuru.

Ya tabbatar wa al-ummar jihar cewa ma’aikatar ta shirya tsaf don tabbatar da samar da sauyi da ci gaba da don samar da ayyuka cikin ingantaccen yanayi yayin da take karfafa dorewar kula da muhalli, sauyin yanayi, da ingantacciyar hanya don sarrafa albarkatun ruwa.

SolaceBase ta ruwaito cewa kwamishinan ya kara da cewa tawagarsa ta himmatu wajen aiwatar da manufofi da shirye-shirye da suka dace da ajandar ci gaban gwamnatin Gwamna Yusuf kuma za su taimaka wa ci gaba da walwalar jihar baki daya.

Ya sake jaddada kudurin ma’aikatar na karfafa kokari wajen magance matsalolin muhalli, inganta samun albarkatun ruwa, da habakar ci gaba mai dorewa a fadin Jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here