Shahararren mawakin Hausa Dauda Adamu Kahutu wanda aka fi sani da Rarara, ya soki tauraruwar Afrobeats, Davido kan yadda ya daga batun daliban da aka yi garkuwa da su a wajen bikin shirye-shiryen fara gasar Kofin Duniya ta 2026.
Wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Rarara ya zargi mawakin da nuna Najeriya ta mummunar hanya a gaban duniya ta hanyar sa rigar da aka rubuta “Bring Them Home” tare da sunayen daliban makaranta da malamai da aka yi garkuwa da a daga Jihar Oyo.
Davido ya yi waka a taron sannan daga baya ya bayyana a shafukan sada zumunta cewa ya yi amfani da dandalin ne don jawo hankalin wadanda abin ya shafa tare da nuna goyon baya ga iyalansu.
“Daga Najeriya zuwa duniya, koyaushe zan wakilci mutanena cikin alfahari,” mawakin ya rubuta, sannan ya kara da cewa yana addu’a ga wadanda abin ya shafa, iyalansu da zaman lafiya a kasar.
Amma a martanin Rarara kan lamarin, mawakin da aka sani da goyon bayan jam’iyyar APC ya ce bai kamata a yi amfani da batun tsaro ta hanyar da za ta lalata sunan kasa ba.
“Abin da Davido ya yi dabbanci ne,” in ji shi. “Ta yaya za ka dauki batun tsaron kasa mai hadari ka nuna shi ga duniya ta hanyar da za ta lalata sunan kasa?”
Mawakin ya yi zargin cewa bai kamata a juya rashin tsaro ya zama abin da za ayi amfani da shi a siyasa ba, inda ya zargi wasu mutane da yin amfani da irin wadannan lamura don samun riba ta siyasa.
Rarara ya tambayi dalilin da yasa Davido ya sanya sunayen daliban da aka yi garkuwa da su a babban dandalin duniya, yana mai nuna cewa lamarin na iya samun tasirin siyasa.
A cewarsa, an yi garkuwa da daliban Oyo ne bayan jami’an tsaro sun kama wasu ‘yan ta’adda da ake zargi, waɗanda ake zargin sun yi garkuwar ne domin tilasta wa gwamnati ta saki wadanda ke tsare.
“Shugaban kasa da jami’an tsaro sun yi alkawarin cewa ba za a saki ’yan ta’addar ba kuma za a ceto yaran. A wannan lokacin ne Davido ya zabi ya kunyatar da mu a babban dandalin duniya,” in ji shi.
A martanin da yayi a shafin X, Davido ya sa rubutun Rarara sannan ya rubuta “Debidooo,” wanda ya bayyana kamar yana yin ba’a kan yadda ake kiran sunansa da Hausa.
Davido ya sake cewa: “Da ace kana da ilimi da na tsaya nayi magana dakai. Amma babu abin da ka sani, sakarai kawai.”
Rikicin ya ci gaba da haifar da muhawara a shafukan sada zumunta, inda magoya bayan mawakan biyu ke bayyana ra’ayoyi daban-daban kan ko daga batun rashin tsaro a babban dandalin duniya yana taimakawa ko yana lalata sunan Najeriya.












































