Majalisar Wakilai ta shiga rudani a zamanta na ranar Laraba, bayan da ’yan majalisar suka samu sabani kan wani kuduri na neman gayyatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu game da yadda ake aiwatar da kasafin kudin shekarar 2025.
Rikicin ya barke ne yayin zaman majalisar, bayan da Benedict Etanabene, dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Okpe, Sapele da Uvwie daga Jihar Delta, ya tayar da maganar wata wasika mai kwanan wata 29 ga watan Yuni, wadda Babban Akanta Janar na Tarayya, Shamseldeen Ogunjimi ya fitar.
Wasikar ta umarci dukkan ma’aikatun gwamnatin tarayya, sassa da kuma hukumomi da su dakatar da fitar da kudaden ayyukan mazabu da na yankuna, har sai Ma’aikatar Ayyuka ta Musamman ta duba ingancin ayyukan.
Etanabene ya bukaci majalisar da ta gayyaci Tinubu domin ya bayyana dalilin jinkirin aiwatar da kasafin kudin na 2025, yana mai gargadin cewa wannan wasika za ta kara dakile aiwatar da Dokar Kasafin Kudi.













































