Your message has been sent
Your message has been sent
Rahotonni sun ce, gwamnatin Akwa Ibom, ta hana ma’aikatan gidan Talabijin na Channels shiga cibiyar yada labaran gidan gwamnati da ke Uyo, babban birnin jihar.
Dakatarwar da aka yi wa Christopher Moffat da kuma Kufre Ikpe wakilin Channels TV da mai daukar hoto daga cibiyar ya biyo bayan yaɗa wani faifan bidiyo inda a cikinsa gwamnan jihar Umo Eno, ke tabbatar da shirinsa na sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Da ya ke magana a taron majalisar zartarwa na jihar a ranar Alhamis, Eno ya bayar da misali da rigimar cikin gida a cikin jam’iyyar PDP a matsayin dalilin da ya sa ya yanke wannan shawarar.
Gwamnan ya kuma bukaci kwamishinonin sa da sauran masu rike da mukaman siyasa da su sauya sheka tare da shi zuwa jam’iyyar APC ko kuma su yi murabus daga mukamansu.
Ya ce, masu rike da mukaman siyasa da ke son ci gaba da zama a PDP suna da ‘yancin yin hakan, amma ba a matsayinsa na ‘yan majalisar zartaswarsa ba.
Kamar yadda PREMIUM TIMES ta ruwaito, Udoh ya kira wakilin gidan talabijin din na Channels cewa gwamnan ya hana shi da mai daukar hotonsa shiga cibiyar manema labarai.
Haka kuma, rahotonni sun ce, Moffat ya kasance wakilin tashar ta Channels a gidan gwamnatin Akwa Ibom, da ke birnin Uyo na sama da shekaru 10.













































