Gwamnatin Kano da hukumar NAGGW za su hada kai don inganta muhalli

WhatsApp Image 2025 05 25 at 10.48.20 750x430

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirye-shiryen zurfafa hadin gwiwa da hukumar kula da bunƙasa muhalli ta Najeriya watau National Agency for the Great Green Wall NAGGW, domin ci gaba da kokarin farfado da filaye da kuma jure yanayi a jihar.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da kwamishinan muhalli da sauyin yanayi, Dakta Dahir M. Hashim, ya sanya wa hannu a ranar Asabar.

Dakta Hashim, wanda ya karbi bakuncin Darakta Janar na hukumar ta NAGGW, Malam Saleh Abubakar, a ofishinsa, ya ce sun tattauna muhimman batutuwan hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da kuma hukumar.

Solacebase ta ruwaito cewa tattaunawar ta ta’allaka ne kan ci gaba da tsare-tsare na muhalli da nufin dakile sauyin yanayi da farfaɗo da ƙasar noma.

A cewar Kwamishinan, ya tattauna da Malam Abubakar kan wasu ayyuka da ake gudanarwa a jihar a halin yanzu, wadanda suka hada da shirin dashen bishiyu guda miliyan 5 da kuma shirin noman rani, wanda ke mayar da garuruwan da ke fadin jihar zuwa korayen wuraren.

Ya kuma bayyana amincewar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a baya-bayan nan na kara albashin jami’an gadin dazuzzuka da kuma daukar karin ma’aikata a kokarin da ke da nufin kara karfafa ayyukan kare muhalli a jihar.

Dokta Hashim ya lura cewa shugaban na NAGGW, ya nuna matukar sha’awar hada kai kan aikin noma da kuma wani sabon shiri na dasa itatuwan dabino miliyan 5 a wani bangare na dabarun kiyaye kasa.

Ya jaddada kudirin jihar na tallafa wa dabarun hadin gwiwa da za su karfafa sauye-sauye musamman a fannin sauyin yanayi da inganta ci gaban jihar Kano, mai dorewa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here