Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa za ta shiga haɗaka da jam’iyyar ADC domin tunkarar zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa. Wannan na daga cikin shirye-shiryen da jam’iyyar ke yi gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Ladipo Johnson, ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wata hira da ya yi a tashar talabijin ta Channels, inda ya yi bayani kan shirye-shiryen jam’iyyar duk da sauye-sauyen da ke faruwa a cikinta.
Ya bayyana cewa duk da ficewar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, NNPP za ta ci gaba da tsayawa takara a zaɓe mai zuwa.
Sai dai a matakin shugaban ƙasa, jam’iyyar za ta yi aiki tare da ADC, yayin da za ta tsayar da ‘yan takara a sauran matakai.
Johnson ya ƙara da cewa an gudanar da tattaunawa da dama tsakanin shugabannin ‘yan adawa kafin Kwankwaso ya yanke shawarar komawa ADC.
Ya kuma jaddada cewa wannan mataki ba zai kawo ƙarshen NNPP ba, domin jam’iyyar na da tsarin da zai ba ta damar ci gaba da aiki.
Ya bayyana cewa haɗin kan da ake ƙoƙarin yi tsakanin jam’iyyun adawa yana nufin samar da wata hanya ga ‘yan Najeriya domin samun madadin shugabanci a zaɓen 2027.
Ya kuma tabbatar da cewa Kwankwaso zai kammala rajista a matsayin ɗan jam’iyyar ADC a Kano a wannan rana.
Rahotanni sun nuna cewa wannan mataki na zuwa ne bayan shafe makonni ana tattaunawa tsakanin Kwankwaso, shugabannin tafiyar Kwankwasiyya da manyan jiga-jigan ADC, domin kafa haɗin gwiwa mai ƙarfi da zai iya ƙalubalantar APC a matakin tarayya.
A baya-bayan nan, an samu rashin jituwa tsakanin Kwankwaso da gwamnan Kano, Abba Yusuf, wanda aka dade ana ganin yana daga cikin manyan mabiyansa.
Ficewar Yusuf daga NNPP zuwa APC tare da wasu ‘yan majalisa da jami’an gwamnati ya kara fito da sabani a cikin tafiyar Kwankwasiyya.













































