Da Dumi-Dumi: Kotu ta hana Aminu Ado Bayero da wasu mutane 4 gabatar da kansu a matsayin sarakuna

kotu, hana, tshon, sarkin, kano, masarautu, rano, karaye, bichi, gaya
Wata babbar kotu a jihar Kano ta umarci tsohon Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da ya daina bayyana kansa a matsayin sarki sannan kuma ya umarci...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Wata babbar kotu a jihar Kano ta umarci tsohon Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da ya daina bayyana kansa a matsayin sarki sannan kuma ya umarci kwamishinan ‘yan sanda da ya kore shi daga karamar fadar jihar.

Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa kotun karkashin jagorancin mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta ba da umarnin a ranar Litinin, 27 ga watan Mayu, 2024.

Karin labari: Gwamnan Kano ya nada mukaddashin manajan daraktan ARTV

Haka zalika, umarnin ya hana Alhaji Nasiru Ado Bayero da Dakta Ibrahim Abubakar II da Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa da Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya su gabatar da kansu a matsayin sarakunan Bichi, Gaya, Rano, da kuma Karaye.

Karin bayani na tafe…

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here