
Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Hajiya Hauwa Isa Ibrahim a matsayin mukaddashin Manajan Darakta na gidan talabijin na Abubakar Rimi (ARTV).
SolaceBase ta rawaito cewa nadin ya biyo bayan dakatarwar da aka yi wa manajan darakta Mustapha Indabawa.
Karin labari: Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta roki Shugaba Tinubu ya shiga tsakanin rikicin masarautar Kano
Wasikar nadin mai kwanan wata 27 ga watan Mayu 2024, ta samu sa hannun Abdullahi Baffa Bichi, sakataren gwamnatin jihar.
Wasikar ta umarce ta da ta karbe harkokin gidan rediyon nan ta ke.
Har zuwa nadin nata, Hajiya Hauwa Isa Ibrahim ita ce mataimakiyar darakta a gidan talabijin na Abubakar Rimi.