A yau Talata ne Allah ya yi wa mahaifiyar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, rasuwa Malama Fatima.
An dai sace Dadiyata ne sama da shekaru biyu da suka babata a gidansa da ke unguwar Barnawa a cikin garin Kaduna.
A cewar Dateline Nigeria, ta rasu ne yau a a Asibitin runduna ta 44 ta sojojin Najeriya da ke Kaduna inda aka kai ta sakamakon rashin lafiya da ba a bayyana ba.
Dadiyata, malami a jami’ar Tarayya da ke Dutsen-Ma, ya bace tun lokacin da aka sace shi, kuma ‘yan uwansa suna rayuwa bisa rashin tabbas game da makomarsa.












































