JOHESU ta sanar da fara yajin aikin sai Baba-ta-gani

JOHESU Strike

Gamayyar ƙungiyoyin ma’aikatan kiwon lafiya ta ƙasa JOHESU, ta bayyana fara yajin aikin gama-gari ba tare da ƙayyadadden lokaci ba, sakamakon jinkirin da gwamnatin tarayya ta yi na tsawon shekaru 12 wajen aiwatar da tsarin albashi na (CONHESS) da aka sabunta.

A cewar shugabanta na ƙasa, Kabiru Ado Minjibir, wannan mataki ya fito ne daga zaman ƙara-ɗaukar matakin da majalisar zartarwa ta faɗaɗɗa ta ƙungiyar ta gudanar a Abuja domin tattauna matsalolin da suka dade suna dawainiya da ma’aikatan.

Ya ce sakamakon wannan zama ya haifar da matsaya ɗaya tilo, wadda ta umarci dukkan ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin ƙungiyar a cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnatin tarayya da su dakatar da ayyukansu nan take daga tsakar darem ranar Juma’a.

A cewar ƙungiyar, wannan mataki ya zama dole ne domin tilasta gwamnatin tarayya ta magance batutuwan da suka shafi tsarin albashi da jin daɗin ma’aikata, wadanda suka yi tsawon lokaci suna jiran aiwatarwa ba tare da ci gaba ba.

Ƙungiyar ta bayyana cewa rashin ɗaukar mataki daga ɓangaren gwamnati ya haifar da gagarumin rashin kwarin gwiwa ga ma’aikatan kiwon lafiya, wanda hakan ya sa suka amince gaba ɗaya cewa babu wani zaɓi illa a tafi yajin aiki.

Ta ce aiwatar da tsarin albashi mai inganci da kuma gyare-gyare a fannin lafiyar jama’a na da matuƙar muhimmanci wajen inganta ayyukan kiwon lafiya da tsare ma’aikata.

Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da sa ido kan lamarin tare da bayyana cewa yajin aikin zai ci gaba har sai an aiwatar da dukkan bukatun da ta gabatar ga gwamnatin tarayya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here