Hukumar Kula da Gidaje ta Taraiya, FHA, ta ce zata dawo da kadaruri da kuma gidadaje da suke karkashin kulawar ta, wanda mutane suka mallaka ba bisa ka’ida ba.
Sanarwara ta kara da cewa hukumar zata fara ati sayen karbo kadarurin ne daga birnin tarayya Abuja da kuma jihar Lagos, saboda a nan ne aka fi samun yawan badakalar.
hukumar ta bayyana cewa akwai tsari da ka’idoji da hukumar take shinfidawa duk wani mutum mai san mallakar gida ko kuma wata kadara dake karkashin kulwar hukumar.













































