Majalisar Wakilai ta janye kudurin dokar ‘yan sandan jiha, tana duba shawarar Tinubu

HOUSE OF REPS MEMBERS 720x430

Majalisar Wakilai ta janye kudurin ta na yi wa tsarin mulki gyaran fuska da nufin kafa ‘yan sandan jiha. Inda take duba wata dokar da ke kama da wannan da bangaren zartarwa ya aiko mata.

Wannan lamari ya bayyana ne a babban taron majalisar na ranar Talata, inda ‘yan majalisar suka karanta kudurin dokar ‘yan sandan jiha da bangaren zartarwa ya gabatar a karatu na farko da na biyu.

Bayan haka, an mika kudurin dokar zuwa ga Kwamitin Majalisar kan Gyaran Tsarin Mulki domin ci gaba da aikin majalisa.

Wannan shawara ta dakatar da tsohon kudurin da majalisar ta gabatar a baya, yayin da hankalin ‘yan majalisar ya karkata zuwa ga gyaran fuskar da bangaren zartarwa ke marawa baya.

Ana sa ran kudurin na bangaren zartarwa zai fuskanci bincike daki-daki a matakin kwamiti, inda ‘yan majalisar za su duba muhimman tanade-tanaden sa kafin a mayar da shi gaban majalisar don ci gaba da mahawara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here