Ramadan: Kada ku yi amfani da gurbatattun kaya wanen sadaka – Malami ga Musulmai

Ramadan Box 512x430

Babban Limamin Jami’ar Jihar Legas, Farfesa Amidu Sanni, ya bukaci al’ummar Musulmi da su ci gaba da da’a, da kyautatawa da kuma bayar da agaji yayin da aka fara azumin watan Ramadan.

Malamin ya ce, da’a da kuma bayar da sadaka ga mabukata su ne alamomin watan Ramadan.

Sanni ya bayyana hakan a zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Legas ranar Asabar.

Karanta: Ramadan: KAROTA ta fitar da wasu ka’idojin tuki lokacin Azumi 

Malamin ya taya al’ummar musulmi murnar shigowar azumin watan Ramadan, inda ya bayyana watan a matsayin lokacin tsarkake ruhi, yana mai cewa azumin ba wai kawai kamewa daga abinci, sha da mu’amalar jima’i daga ketowar alfijir zuwa faduwar rana ba. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here