Ana zargin ’yan bindiga sun sace dalibai bakwai na Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Tarayya, Kaura Namoda, Jihar Zamfara.
An yi garkuwa da daliban ne a gidajen kwanansu da ke wajen makaranta gefen garin Low-Cost na Kaura Namoda.
Shugaban Karamar Hukumar Kaura Namoda, Hon. Mannir Haidara Kaura, ya tabbatar da da faruwar lamarin a ranar Laraba.
Ya ce hukumomin tsaro sun fara aikin ceto domin tabbatar da dawowar daliban da aka yi garkuwa da su cikin aminci.
Daya daga cikin daliban makarantar, Ibrahim Ahmad, ya bayyana cewa daya daga cikin daliban da aka sace ya samu nasarar tserewa, inda aka bar dalibai maza uku da mata uku a hannun masu garkuwa.
A halin da ake ciki, wata kungiya mai suna Concerned Citizens of Kaura Namoda ta bayyana damuwa kan abin da ta kira tabarbarewar matsalar tsaro a yankin, wadda ake zargin wani fitaccen shugaban ’yan bindiga, Kachalla Bello Dansadiya da jama’arsa ne ke aikatawa.
A cikin sanarwar, kungiyar ta bayyana abubuwan da suka faru a baya, ciki har da sace manyan malamai biyu aka kuma tsare su kusan watanni biyu duk da an biya kudin fansa.












































