Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ta bude dandali don neman aikin soja na musamman wato Short Service Combatant Commission Course 50/2027 ga ‘yan Najeriya da suka cancanta, cikin har da fararen hula da kuma jami’an da ke aiki a halin yanzu.
A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ranar Talata, ta bayyana cewa wadanda suka yi nasara za a ba su mukami a bangaren yaki da kuma bangaren tallafawa yaki na rundunar sojin kasan Najeriya.
Ta ce bangaren yaki ya kunshi dakarun kasa da dakarun tankokin yaki, yayin da bangaren tallafawa yaki ya hada da dakarun manyan bindigogi, injiniyoyi, sadarwa da kuma sashen binciken sirri.
“Ana bukatar masu sha’awar neman aikin da su rika tura takardunsu ta sahihin shafin yanar gizo na daukar ma’aikata na Rundunar Sojin Kasa nashortservice.army.mil.ng.
“Ana shawartar masu neman aikin da su zabi bangaren SSCC a dandalin, sannan su bi umarnin da aka bayar daki-daki da taka-tsantsan,” in ji sanarwar.
Rundunar sojin ta yi gargadi ga masu neman aikin da su yi watsi da duk wasu shafukan yanar gizo ko sanarwar daukar ma’aikata na bogi wadanda ba su da izini, tana mai karfafa musu gwiwa da su dogara kacokan da sahihan hanyoyin sadarwa na Rundunar Sojin Kasa kadai domin samun ingantaccen bayani.
Haka kuma ta karfafa gwiwar masu neman aikin da su rika lura da tallace-tallacen sanarwar daukar ma’aikatan a gidajen talabijin da na rediyo biyo bayan fitar da wannan sanarwa.
“Ranar Asabar, 17 ga watan Oktoba, 2026 ce ranar karshe.
“Domin neman karin bayani, masu nema za su iya kiran wadannan lambobi: 07016874003 ko 07047340295 tsakanin karfe 8 na safe zuwa karfe 6 na yamma kowace rana,” in ji ta.
Rundunar sojin ta yi kira ga kowane dan Najeriya da ya cancanta kuma yake da sha’awar yi wa kasarsa hidima da ya yi amfani da wannan dama kafin cikar wa’adin da aka deba na neman aikin. (NAN)













































