Gobara ta ƙone wani coci ƙurmus a Legas

Gobara, coci, legas, kone
Wata gobara ta kone wata fitacciyar majami'a da ke Legas da aka fi sani da gidan David a lokacin da ma'aikata ke kokarin shirya wa wani taro...

Wata gobara ta kone wata fitacciyar majami’a da ke Legas da aka fi sani da gidan David a lokacin da ma’aikata ke kokarin shirya wa wani taro.

Gobarar ta faru ne da safiyar jiya Laraba sa’oi kafin cocin ya soma wani taron shekara-shekara da yake samun halartar matasa da manya.

Wasu ma’aikata na aikin shirya dakin taron lokacin da suka gano wuta na tashi daga rufin ginin.

Karanta wannan: Za mu sauya fasalin kasuwar tsohuwar Fanteka – Uba Sani

Wani shaida ya fada wa yan jarida cewa gobarar ta soma ne daga rufin ginin inda kuma ta gone wajen kurmus.

Shaidan ya ce a kan idonsu wutar ta kone kayan kide-kide da na’urarorin sanyi saboda ba za su iya yin komai ba saboda wutar da ke tashi gagga-gagga.

Sashen BBC Pidgin ya rawaito yadda gobarar ta kone ginin baki daya inda yanzu ya zama toka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here