Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin cewa zai dawo da tsarin tallafin mai, inda ya ce kudin da aka samu daga cire tallafin da Shugaba Bola Tinubu ya yi an “sace” su.
Atiku, a wata hira da ya yi da ‘yan jarida a ranar Laraba, ya ce duk da cewa bai yi adawa da cire tallafin ba, amma kudin da aka ce an samu daga wannan tsarin an sace su kuma ba a sake saka su ba domin inganta rayuwar ‘yan kasa.
“Ban yi adawa da cire tallafin ba. Amma ina kudin? Kudin da aka samu ya kamata a yi amfani da shi wajen magance talauci, yaran da basa zuwa makaranta da sauran abubuwa,” in ji Abubakar.
Tsohon Mataimakin Shugaban ya kara da cewa “Ina kudin? Sun sace shi. Zan dawo da tallafin mai. Babban abin shi ne sun cire tallafin, amma ina kudin? Ko da ni ne na cire tallafin, har yanzu zan yi aiki.
An cire tallafin ne domin inganta ilimi, tsaro, talauci da sauran abubuwa, saboda haka zan dawo da tallafin.”
Ba a samu damar jin ta bakin Fadar Shugaban Kasa ba kan zargin da ya yi na cewa an sace kudin tallafin mai.
A cewar Abubakar, ya yi magana da tsoffin shugabannin NNPC 5 wadanda suka yarda cewa yana da gaskiya kan matsayarsa game da tallafin mai.
“Wani abu ya faru makon da ya gabata. Shugabannin NNPC 5 da suka gabata sun kira ni suka ce, ‘Ba mu yarda da shirin ka ba lokacin da ka fitar da shi, amma yanzu mun yarda.’ Sun ce su ne suka yi kuskure, ba ni ba. Har sai ka samu mulki, irin wadannan abubuwa ba za a iya yi ba,” in ji Mista Abubakar.












































