Shugaban Kasa Bola Tinubu ya gana da Shugaban Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Olanipekun Olukoyede da Ministan Gidaje da Raya Birane, Muttaqha Rabe Darma, kan batun kula da sayar da gidaje da sauran filaye da gwamnatin tarayya ta kwace.
Ganawar, wanda aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Talata, ta mayar da hankali ne kan yadda za a kula, kiyaye da kuma sayar da kadarorin da aka kwace ta hanyar shari’o’in yaki da cin hanci da rashawa da laifukan kudi, daidai da sharuddan gaskiya da rikon amana.
Wannan taro ya zo ne sakamakon karuwar yawan filaye da gine-gine da EFCC ta kwace ta hanyar umarnin kotu na wicin gadi da na matakin karshe a fadin kasar.
Ganin Shugaba Tinubu, shugaban EFCC da Ministan Gidaje ya nuna yadda gwamnatin ke son wuce batun kwato kadarori kadai, zuwa tabbatar da cewa an kula da su yadda ya kamata kuma an yi amfani da su don amfanin al’umma.
Wata babbar kadara da aka riga aka mika wa Ma’aikatar Gidaje ita ce rukunin gidaje mai guda 753 da ke fuloti mai lamba 109, Cadastral Zone C09, gundumar Lokogoma, Abuja.
Rukunin gidajen, wanda ya kunshi rukunoni daban-daban da dakunan zama a kan fili mai fadin murabba’I 150,000, kotu ta bada umarnin kwace shi tare da baiwa Gwamnatin Tarayya a watan Disamba na shekarar 2024.
Daga baya, EFCC ta mika rukunin gidajen ga Ma’aikatar Gidaje da Raya Birane ta Tarayya a watan Mayu na shekarar 2025 domin kammalawa da kuma tura su don amfanin jama’a.
An ce rukunin gidajen yana da alaka ne da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Sauran kadarorin da ke da alaka da Emefiele wadanda ke fuskantar shari’ar kwacewa sun hada da duplexes da apartments a Lekki Phase 1 da Ikoyi, filaye da ba a gina ba da wani babban gida (bungalow) a kusa da Queens Drive, Ikoyi, kadarori a kan titin Probyn Road da Adekunle Lawal Road da wani babban rukunin masana’antu da ya mamaye filaye 22 a Agbor, Jihar Delta.
Kadarorin sun kuma hada da wani babban gini mai hawa da dama wanda ke dauke da gidaje da dama a yankin Otunba Elegushi a Legas, gine-ginen masana’antu da rumbunan ajiya, da sauran filaye da rukunonin gidaje a Lekki, Ikoyi da Amuwo-Odofin.
Har ila yau, a shekarar 2026 da muke ciki, Kotun Koli ta tabbatar da kwace wasu kadarori bakwai da ke da alaka da Emefiele, tare da kudade da sauran kadarori.
Yawan kadarorin da aka kwace ya kara fadada a wannan shekarar sakamakon shari’ar da ta shafi tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Kasa, Abubakar Malami, abokansa, iyalansa da kamfanoninsa.
An bayar da umarnin kwacewa na wucin gadi kan kadarori 57, wanda darajarsu ta kai kimanin Naira biliyan 213 a watan Janairu. A watan Yuli kuma, an kwace kadarori 48 da darajarsu ta kai Naira biliyan 180, yayin da aka saki guda tara.
Alkaluman da ke akwai sun nuna irin girman kalubalen kula da kadarorin da ke gaban Gwamnatin Tarayya, inda EFCC ta bayar da rahoton kwato kadarori fiye da 1,500 wadanda ba na kudi ba (mafi yawancinsu gidaje da filaye) tsakanin ƙarshen 2023 zuwa 2025.
To sai dai kuma, matsayin kadarorin ya bambanta dangane da shari’a. Yayin da wasu kotu ta bayar da umarnin kwace su na karshe ga Gwamnatin Tarayya, wasu kuma suna karkashin umarnin kwace na wici-wici ne, kuma har yanzu ana iya yin kalubale, daukaka kara, ko sauran hanyoyin shari’a a kansu.
Don haka, ana sa ran taron zai karfafa hadin gwiwa tsakanin EFCC da Ma’aikatar Gidaje wajen kula da wadannan kadarori da ke kara yawa.
Hukumar EFCC ce ke samun umarnin kwace kadarori kuma ta mallake su, yayin da Ma’aikatar Gidaje ke da kwarewar aiki na aunawa, kammalawa, gudanarwa, ko tura kadarorin gidajen da aka mika wa gwamnati don amfanin jama’a.













































