Shugaba Buhari ya kaddamar da sabon kamfanin mai na kasa

NNPC Unveiling 750x430 1
NNPC Unveiling 750x430 1

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon kamfanin mai na kasa wanda aka sauya wa fasali, inda a yanzu kamfanin na NNPC ya koma karkashin gudanarwar ‘yan kasuwa.

An yi kaddamarwar ne a wani kwarya-kwaryan biki da aka gudanar a Abuja babban birnin kasar .

Shugaba Buhari ya fara ne da gode wa mahartar taron, wanda ya kira shi da ”mai dimbin tarihi”.

A jawabin da ya gabatar a wurin taron, shugaba Buhari ya ce an mayar da ikon gudanar da kamfanin ga ‘yan kasuwa ne, saboda inganta shi, don samar wa kasar makashin da take bukata.

Ya kuma kara da cewa ”daga yanzu kamfanin NNPC ya koma karkashin gudanarwar ‘yan kasuwa, zai kasance kamfani mai zaman kansa ta yadda zai yi gogayya da takwarorinsa a fadin duniya, domin ci gaba da bunkasa hannayen jari sama da miliyan 200 tare da habaka fannin makashi a fadin duniya”.

”A yanzu doka ta dora wa kamfanin alhakin tabbatar da samar wa Najeriya wadataccen makashin da take bukata domin samun habakar tattalin arzikin ta hanyar farfado da wasu fannonin da ke bukatar makashin”. in ji Shugaba Buhari.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here