ASUU ta musanta karbar naira biliyan 52 daga gwamnatin tarayya

84379EF8 DF67 418B B072 D88C667DAB71
84379EF8 DF67 418B B072 D88C667DAB71

Kungiyar malaman jami’o’i ta Nigeria ASUU ta musanta karbar tsabar kudi har naira biliyan 52 daga gwamnatin tarayya.

Ministan kwadago Chris Ngige ne ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta fitar da domin biyan malaman jami’an bashin alawus da albashi na fiye da watanni 20 da suke bin gwamnatin.

Da yake zantawa da ‘yan jarida Shugaban kungiyar ta ASUU shiyar Kano Farfesa Abdulkadir Muhammad ya ce, kungiyar ta karbi naira biliyan 22 daga gwamnatin tarayya, suka yi amfani da kaso 75 cikin kudin, yayin da suka raba kaso 25 ga sauran kungiyoyi dake karkashin kungiyar.

Ya kara da cewa labarin da ake yadawa cewa sun karbi naira biliyan 52 karya ne, gwamnati ce ta fito da shi domin batawa kungiyar suna saboda kungiyar ta dage akan sai an kawo gyara a harkar ilimi.

Farfesa Abdulkadir Muhammad ya yi kira da gwamnatin tarayya da tayi kokari wajen kawo karshen matsalar tsaro dake addabar kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here