Rikicin APC Kano: Kotun daukaka kara dage yanke hukunci zuwa gobe juma’a

Kotun daukaka dake babban birnin tarayya Abuja ta dage sauraren karar da jam’iyyar APC bangaren gwamnan Kano Ganduje ya shigar yana  kalubalantar wani hukuncin kotu da ya rusa zaben mazabu da suka gudanar, wanda hakan ya tabbatar da Ahmad Haruna Zago a matsayin Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano.

Tunda fari dai wata babbar kotun tarayya dake zaune a unguwar Maitama dake babban birnin tarayya Abuja ce rusa zaben mazabu na APC wanda bangaren gwamna Ganduje ya gudanar, inda kotun ta tabbatar da zaben da tsagin Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau.

Rashin yadda da wannan hukunci ya sanya tsagin gwamna Ganduje suka daukaka, suna naiman kutun ta tabbatar da zabukan da suka yi, sannan ta ayyana sunan Abdullahi Abbas a matsayin halastaccen Shugaban jam’iyyar APC na Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here