INEC ta fitar da jerin sunayen Yan takarar Shugabancin Kasa 18 da na majalisun Tarayya Sama da dubu 4

INEC Presidential Candidates
INEC Presidential Candidates

Kimanin ‘yan takarar shugaban kasa 18 ne da ‘yan takarar majalisar tarayya dubu 4 da 223 ne suka shiga jerin sunayen ‘yan takarar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta buga a ranar Talata.

A ranar Talata ne hukumar zaben ta fitar da jerin sunayen bayan taron ta na mako-mako da ta gudanar a hedikwatar ta ta kasa da ke Abuja.

Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye, ya ce an buga jerin sunayen ne kamar yadda “sassa na 32(1) da na 8 na dokar zabe ta 2022 ya tanada”.

A ranar 4 ga watan Oktoba ne za a buga jerin sunayen ‘yan takarar gwamna da na ‘yan majalisun jihohi na karshe.

Da yake bayani kan sunayen da aka buga, Okoye ya ce: “A takaice dai, dukkanin jam’iyyun siyasa 18 sun tsayar da ‘yan takara da abokan takararsu a zaben shugaban kasa. A zaben ‘yan majalisar dokoki, ‘yan takara dubu 1 da 101 ne ke neman kujeru 109 na Sanatoci sai kuma ‘yan takara majalisar wakilan Tarayya dubu 3 da 122, wanda jimlar ‘yan takara dubu 4 da 223 ne ke neman kujeru 469 na majalisun biyu.

A bangaren rabon jinsi kuwa, ‘yan takara dubu 3 da 875 maza ne, wadanda suka kunshi 35 na shugaban kasa da mataimakansu, dubu 1 da 8 na majalisar dattawa da Kuma dubu 2 da 832 na majalisar wakilai.

“Hakazalika, mata Dari 381 da suka kunshi 1 na Shugaban kasa, 92 na Majalisar Dattawa, da 288 na Majalisar Wakilai ne ke takara.

Akwai kuma Mutane 11 masu bukata ta musamman (PWDs) a cikin Yan takarar.

Ana buga jerin sunayen mazabu a kowace Jiha inda suke yayin da aka shigar da cikakken jerin sunayen na kasa baki daya a shafin Hukumar na Internet.”

A halin da ake ciki kuma, a jerin sunayen ‘yan takarar majalisar dokokin kasar da INEC ta wallafa, ba a ga sunan shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ba.

Hukumar ba ta bayyana sunan ko wanne dan takarar jam’iyyar APC a bangaren masu neman kujerar Sanatan Yobe ta Arewa ba.

Hukumar ta INEC ta ce ta dauki wannan matakin ne kamar yadda ta bayyana a baya cewa ba za ta amince da duk wani dan takarar jam’iyyar APC a zaben Sanatan yankin ba sakamakon rikicin da ya biyo bayan tikitin takarar sanatan APC na Yobe ta arewa bayan APC ta mika sunan Lawan ga INEC maimakon Bashir Machina da ya lashe zaben fidda gwanin da hukumar ta sanyawa ido.

Za a iya saukar da cikakken jerin sunayen ‘yan takarar shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar nan a adireshin dake Kasa….

Final-List-of-Candidates-for-National-Elections-1

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here