Wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai, a ranar Talata, sun kai hari a wani masallaci a Gusau da ke babban birnin jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da wasu masu ibada.
Kamar yadda SOLACEBASE ta rawaito, an kai harin ne a lokacin da mabiya addinin Islama ke gudanar da sallar jam’i ta Tahajjud cikin tsakar daren watan azumin ramadan.
Karin labari: An kashe mutane 2 da kone gidaje a rikicin kabilanci a jihar Benue
Tahajjud addu’a ce ta musamman da musulmi ke gudanar da ita a kowane kwanaki 10 na karshen watan Ramadan.
Cikakken bayanin na nan tafe…