Dakarun tsaro na haɗin gwiwa a ƙarƙashin aikin Operation MESA sun ceto mutane uku daga cikin biyar da aka sace a wani harin ‘yan bindiga da aka kai da dare a ƙaramar hukumar Gwarzo ta jihar Kano.
Aikin ceton ya haɗa da sojojin Brigade ta 3 na Rundunar Sojin Ƙasa ta Nijeriya, tare da haɗin gwiwar Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya da Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, domin bin sawun ‘yan bindigar da suka kai harin.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa sabon harin da aka kai a garin Lakwaya da ke ƙaramar hukumar Gwarzo ya samu tabbaci daga dagacin ƙauyen Zurin Mahauta, Murtala Mai Unguwa.
Labari mai alaƙa: ’Yan bindiga sun sace mutane 7 a wani sabon hari suka kai a Kano
Mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na Rundunar Sojin Ƙasa, Brigade ta 3, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya tabbatar da nasarar aikin ceto ga jaridar Solacebase.
Ya bayyana cewa an samu nasarar ceto mutane uku cikin aminci, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kubutar da sauran mutane biyu da ke hannun masu garkuwa da mutane.
Ya ƙara da cewa dakarun da ke cikin aikin sun kuduri aniyar tabbatar da dawowar dukkan mutanen da aka sace cikin koshin lafiya, tare da ba jama’a tabbacin cewa aikin tsaro zai ci gaba har sai an kammala ceto gaba ɗaya.













































