Yan majalisar Wakilai a Najeriya yanzu haka sun fara tantance hafsoshin tsaro da shugaban kasa Bola Tinubu ya nada a kwanakin baya.
Daga cikin hafsoshin tsaron akwai Christopher Musa, Hafsan tsaro da Taoreed Lagbaja wanda shi ne shugaban sojin kasa sai Emmanuel Ogalla hafsan sojin ruwa sai kuma Hassan Abubakar a matsayin hafsan sojin sama.
A makon jiya ne Shugaba Tinubu ya tura sunayensu don tantance su a majaliasar.