‘Yan Sandan Najeriya sun ceto Mrs Olaide Busayo Adegoke John-Paul da tagwayenta maza masu shekara 12, Peter da Paul, a raye yayin wani aikin ceto da aka gudanar da misalin karfe 7:30 na yamma ranar Asabar.
Majiyarmu daga hedkwatar ‘yan sanda, ta ce an kashe mutum 2 cikin masu garkuwa da ake zargi yayin musayar wuta da jami’an ‘yan sanda, sannan an kwato bindigu 2 daga hannun ‘yan bindigar.
An yi garkuwa da wadanda aka ceto, ciki har da kanwar tsohon Ministan Lantarki, Cif Adebayo Adelabu, da misalin karfe 7:30 na safe a ranar 3 ga Yuni 2026, yayin da suke kan hanyarsu ta kai yaran makaranta a Ibadan, Jihar Oyo.
Majiyoyin ‘yan sanda sun bayyana cewa binciken sirri da matsin lamba na dabaru sun tilasta wa masu garkuwar fuskantar jami’an ‘yan sanda, lamarin da ya kai ga ceto wadanda aka sace cikin nasara.
Majiyar ta ce jami’an tsaro har yanzu suna sintiri a yankunan da ke kusa don neman sauran mambobin kungiyar masu garkuwar, wadanda ake ganin wasu sun gudu da raunukan harbi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar don tabbatar da an sace ta, mai magana da yawun Adelabu, Femi Awogboro, ya ce an sace su da misalin karfe 7:30 na safe yayin da Mrs John-Paul take kai yaranta makaranta, lamarin da ya sa iyali cikin damuwa.
“Mun yi matukar kaduwa da wannan mummunan lamari amma muna da kyakkyawan fata cewa za a ceto wadanda aka sace lafiya, muna rokon jama’a su kwantar da hankali, su guji hasashe, su kuma goya wa kokarin jami’anta tsaro baya da ake yi da addu’o’i,” in ji sanarwar iyali.
Ita ce ‘yar karshe cikin ‘ya’ya 5 na Mrs Olufunmilayo Aduke Adegoke Adelabu, wacce ta yi ritaya daga aiki a First Bank Pension Custodian a 2025 kafin ta koma Ibadan tare da yaranta.
An sace su ne ‘yan makonni bayan an sace dalibai da malamai sama da 40 a Karamar Hukumar Orire ta Jihar Oyo, lamarin da ya jawo fushi da zanga-zanga a fadin kasar.












































