Tsohon shugaban tashoshin ARTV da Radiyon Kano Getso ya rasu

1780775718821 750x430

Fitaccen mai ma’aikacin radiyo kuma tsohon Manajan Darakta na Abubakar Rimi Television (ARTV) da Radiyon Kano, Alhaji Adamu Ibrahim Getso, ya rasu yana da shekara 75.

Makusantan marigayin sun ce gogaggen mai gudanar da harkokin yada labarai ya mutu a ranar Asabar bayan doguwar rashin lafiya.

SolaceBase ya rawaito cewa Adamu Getso, ya kasance dan garin Getso ne a Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano, ana mutunta shi sosai saboda shekaru da hidimarsa ga harkokin watsa shirye-shirye da kuma rawar da ya taka wajen inganta sadarwa ga jama’a a jihar.

A tsawon shekarunsa na aikin, ya yi aiki a matsayin Manajan Darakta na Tashar Abubakar Rimi TV a wa’adin farko nagwamnatin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso. Daga baya aka nada shi Manajan Darakta a Gidan Radiyon Kano a wa’adi na biyu na gwamnatin ta Kwankwaso.

Getso ya samu karbuwa sosai a matsayin mai gabatar da shirye-shirye masu tasiri da dama da harshen Hausa, musamman ‘Hukuma da Jama’a’ da ‘Aiki Sai Mai Shi’, wadanda ke mayar da hankali kan manufofin gwamnati, harkokin jama’a, da shirye-shiryen ci gaba.

Abokan aiki, abokan hulɗa, da masoya sun yi ta yima shi yabo, inda suka bayyana shi a matsayin kwarren ma’aikaci mai himma wanda gudummuwarsa ta taimaka wajen tsara ci gaban watsa shirye-shiryen rediyo da talabijin a Jihar Kano.

Marigayin ya bar mata, ‘ya’ya, jikoki, da sauran dangi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here